Anfanin kukumba da dama ga rayuwarmu ta yau da kullum

 

Cucumber tana da sirruka da
dama a tattare da rayuwar dan
adam, domin masana kiwon
lafiya sun bayar da umarnin a
yawaita yin amfani da ita
saboda irin sirrukanta a jiki. Kadan daga cikin amfaninta ga
rayuwarmu ta yau da kullum sun
hada da:
.
1. Narkar Da Kitse: Duk mai yawan amfani da
Cucumber zai rika samun
isasshen lafiya, karin ni’imar jiki
da kwarjini. Wannan ta sa mata
suke yawaita sanya barinta a
kan idanuwansu. Dalili a fili ne cewa a daidai lokacin da mace
ta sanya Cucumber a kan
fuskarta, Cucumber za ta tsotse
duk rubabben kitse da ke tattare
a kan fatar kwayar idanunta
nata, domin tana da wasu sinadaran da ke warkar da irin
wadannan cutukan na kan fata.
Ba ma a fatar idanu kawai ba, an
nuna cewa mutum zai iya gyara
Cucumber ya dora kan duk inda
yake masa ciwo, ko inda fata ta sami matsala. Sannu a hankali
komai zai gushe kuma zai samu
waraka nan take.
.
2. Kore Yana Da Raba: So tari idan mutum ya yi wanka
da ruwan zafi, raba za ta rufe
duk wani gilashin da ke dakin
wankan ko kuma bayan ya fito
zai rasa yadda zai kalli madubi
sabo irin wannan rabar da yana a wasu lokutan. Daya daga cikin
sirrukan Cucumber su ne da arar
ka shafa shi a kan gilashin, daga
lokacin zai washe kuma mutum
ya ci gaba da amfani da kayansa
lafiya lau.
.
3. Ciwon Kai: A duk lokacin da mutum ya sha
wahalar aiki ko gajiyar
musamman, wadanda ke
haddasa nauyin jiki a lokacin da
aka tashi daga bacci, muddin ya
dan ci Cucumber kafin ya kwanta, zai tashi tamkar wanda
ya wuni yana motsa jiki.
.
4. Warkar Da Radadi: A wasu lokutan mutum ya kan
iya samun buguwar wata gaba a
jikinsa, har ta kai shi da yin kara
saboda da radadin da zai iya ji
daga gare shi. Amma a duk
lokacin da ki ka shafa Cucumber a wajen da irin wannan radadin
ya samu, nan da nan radadin da
zafi za su gushe saboda irin
sirrin da ke cikin Cucumber.
.
5. Share Datti A Kan Bango: Kamar yadda muka ambata
Cucumber tana da sirruka daban-
daban bila-adadin, sai dai
mutum ya takaita ga wadanda
ya sani kawai. Ko ka san za ka
iya amfani da ita wajen share kowane irin nau’i na datti ko
zane a bango da yara ke yi da
abin rubutunsu? Da zarar ka bare
Cucumber ka shafe a kan zanen,
zai bace tamkar babu wani
zanen da aka taba yi a wajen.
.
6. Warkar Da Warin Baki: Da yawa daga cikin mutane suna
fama da matsalar warin baki.
Muddin za su yi magana bakinsu
ya rika wari ainun ta yadda ba za
a so matsawa kusa da su ba.
Idan kina da wannan matsalar kawai ki bare Cucumber, ki
sanya a cikin bakinki sai ki rike
shi a daidai saman bakin da
harshe kimamin Sakan 30. Daga
nan ki tofar da ita a kasa. Idan
kika luzumci wannan, warin bakinki zai kau ba tare da bata
lokaci ba.
.
7. Cire Tsatsa: Uwarigda da zarar kin lura a
cikin kayan girkinki akwai
wadanda suka yi tsatsa, maza ki
yi amfani da Cucumber, da zarar
kin yayyanka ta, kika yi amfani
da ita a kan kwanukan. Ba ma goge tsatsar kadai zai yi ba, kin
hutar da kanki da yin amfani da
wasu sinadaran da za su iya
cutar da ‘ya’yanki.
.
8. Karin Kuzari: A duk lokacin da gajiya ta yi miki
yawa, maimakon kwanciya don
ki huta, kawai ki yanka
Cucumber ki ci kadan, za ki
wartsake nan da nan.
.
9. Gyara Fatar Fuska: Ina masu amfani da mayuka
masu lalata fuska ko bata jiki?
Da zarar zarar kin yayyanka
Cucumber kika dora a wuta ya
tausa sosai, kawai ki bude
marfin tukunyar sai ki sanya fuskarki don dumin ruwan ya
shafi fuskarki. Daga nan za ki ga
yadda fuskarki za ta koma ba
tare da wata matsala ba. 10. Wankin Takalmi: Idan kika yayyanka Cucumber, za
ki iya amfani da shi wajen
gyarawa da wanke takalmin
maigida. Yin amfani da ita ba
kawai za ta sanya takalmin yin
sheki ba kawai, za ta tsotse duk ruwan da ke jikin takalmin.