Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Da Zai Wayar Da Kan Jama'a Yadda Za Su Amfana Da Tallafin Naira Biliyan 75 Da Za A Rabawa 'Yan Nijeriya

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Kwamitin da Gwamnatin Jihar Katsina, ta kafa domin wayar da kan alumma Jihar Katsina, ya shirya taro da Shugabannin Kungiyoyi daban daban da kuma kamfanoni masu zaman kansu da ke Jihar Katsina, domin kara fadakar da su kan yadda za su amfana da shiryen shiryen da Gwamnatin Tarayya ta kirkiro domin rage radadin da cutar Corona ta jefa masu kananan sanaaoi da matsakaitan kamfanoni da ta jefa su, wanda zaa raba biliyan sabai'in da biyar.
Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Kuma Shugaban Hukumar Zuba Hannun Jari ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya bayyana dalilin da ya sanya gwamna Aminu Bello Masari ya kafa Kwamitin, domin kara zaburar da ilmantar da al'ummar Jihar Katsina don ganin baa bar Jihar Katsina a baya ba, kan wadannan shirye-shiryen tallafin Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar yi.

Ibrahim Tukur Jikamshi ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya tana so ta Farfado da tattalin arziki da cutar Corona ta jefa masu kananan sanaaoi da makarantu, shi ne ta kirkiro da shirin da ta yi wa lakabi da (Survival Fund) kuma an samu matsalar rashin biyan albashi, Kuma Shirin guda biyar. Akwai tallafin biyan albashi na wata ukku, na maaikaci goma na kowacce masana'anta. Akwai masu harkar Zirga-Zirga, suma zaa ba su tallafi, akwai mutum dubu dari da zaa dubu hamsin. Akwai kuma masu yin takunkunmi da sinadirin wankin hannu, zaa saye kayan da suka sarrafa. Zaa tallafawa mutane Miliyan dari da sabai'in. Idan muka tattauna da ku, mu ka fadakar da ku yadda shirye-shiryen suke, ku kuma ku je ku fadakar da membobin ku, domin ganin sun shiga cikin wadannan shirye-shiryen, kuma dukkanin su ana shigarsu ta hanyar yanar gizo, Kuma sati biyu za'a yi ana cike wannan shiri.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya cigaba cewa ana sa ran jihar Katsina tana da gurabe sama da dubu arba'in, wadanda za su amfana da wannan shirin, mun zauna da jami'in daga hukumar yiwa kamfanoni rijista domin ganin an samu saukin yin rijista. Haka kuma za mu fadakar da shagunan masu yanar gizo a kowacce karamar hukuma da ke Katsina, domin an shamu a baya, a wasu shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya tayi a baya.