.....Kungiyar "Arewa Media Writers" Tana Kira Ga Gwamnatin Nijeriya Da Ta Agazawa Al'ummar Jihohin Da Mummmunar Ambaliyar Ruwan Ya Shafa
Daga Kungiyar Arewa Media Writers
A jiya 08/09/2020 al'ummar jihohin Kebbi Sokoto da Jigawa sun gamu da Iftila'i na ambaliyar ruwan sama, inda ruwan yai barna mai yawa har wasu ma suka rasa rayukansu tare matsugunan su.
Duba da haka kungiyar marubutan Arewa a kafafen sadarwar Zamani "Arewa Media Writers" take kira ga Gwamnonin jihohin dama Gwamnatin tarayya dasu agazawa yankunan da iftila'in ya afku musu.
Ambaliyar ruwan ya jawo wasu al'ummar jihohin sun rasa gidajensu, kayayyakin su da Abincinsu wanda ya hada da Shinkafa, Gero, dadai sauran kayan amfani, inda barnar tafi muni a karamar hukumar mulkin Goronyo, dake kusa da dam din Goronyo a jihar Sokoto, da kuma wasu yankuna a birnin Kebbi, da Jega, Bunza, Yauri, Bagudu, da Makera, dake Jihar Kebbi da wasu yankuna a kananan hukumomin birnin kudu, Jahun, Miga, Da Kuma Taura dake Jihar Jigawa, da dai sauran wasu Jihohin dake yankinmu na Arewa.
Al'ummar yankunan sunce basu taba shiga cikin mawuyacin hali na ambaliyar ruwa kamar na wannan lokacin.
Kungiyar "Arewa Media Writers" ta na sake kira ga gwamnatin Nigeria da ta tallafawa al'ummar yankunan domin rage musu radadin halin da suke ciki.
Haka zalika kungiyar Arewa Media Writers tana jajantawa wa 'yanda ifitila'in ya afuku musu.
Da fatan Gwamnati zata duba domin ganin an ceto al'umma daga cikin wannan musiba Allah yabada sa'a.