An Haramta wa Wasu 'Yan Siyasar Nijeriya Shiga Kasar Amurka

 


 Kasar Amurka ta hana  wasu ƴan siyasar Nijeriya takardar bisar,  Kasan cewar  ta yi zargin cewa wadannan ‘yan siyasan na yi wa harkokin zabe magudi a zabukan gwamnan jihohin Edo da Ondo da ke tafe.

Haka zalika hanawar ya shafin daidaikun mutane da ta zarga cewa sun yi katsalanda a zaben watan Nuwamban 2019 na gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkan, Morgan Ortagus ta fitar, ta ce mutanen da aka sanyawa wannan takunkumi na yiwa “harkokin demokradiya a Nijeriya zagon-kasa ko kuma shirya rigingimun masu alaka da bayan zabe”.

Jami’ar ba ta yi karin haske kan sunayen mutanen da aka sanyawa wannan takunkumi ba, ko adadinsu, da kuma yadda Amurkan ta zabo sunayen mutanen.