Daga Ibrahim Rabilu
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen karamar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara sun kama wata motar roka data fito daga jihar Anambra dauke da miyagun kwayoyi da suka hada da, Tabar wiwi, Kwayoyin kawar da hankali da kudin da kai har na naira milyan 100.
Wadanda kayan an yi hasashen an yi nufin kaisu ne baban birnin jihar Zamfara wato Gusau domin raba su zuwa garuruwa daban daban na jihar Zamfara, Allah ya toni asirin su ne a dai dai shingen hada kar da Jami'an tsaro suka kafa.
Wannan ne baban kamu da miyagun kwayu da aka taba samu a tarihin jihar Zamfara, Nuna wadanan kayan ya samu halarta manyan yan siyasa daga cikin jihar Zamfara, Mai martaba Yandoton Tsafe Emir Of Tsafe, Da iyayen kasa da wakilan Jami'an tsaron yan sanda, Sojoji, Fire service, Zarota, Civil Depence, Hisbah da sauransu.
Lallai wannan babbar nasara ce la'akari da halin da jihar nan ke ciki na rashin tsaro da tashen hankula, Sanin kowa ne shaye shaye duk yana da alaka da wannan miyagun ayyukan.