Ba Za Mu Sassauta Wa ‘Yan Ta’adda Ba, Inji Buratai

 


Shugaban rundunar sojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya zaburar da dakarun rundunar Operation Sahel Sanity da ke yaki da ‘yan bindiga. Buratai ya ce kada su sassauta wa ko tausayawa ‘yan bindigar ko kadan a yakin da suke yi na kawar da ayyukan ‘yan ta’addar a yankin Arewa maso yamma.

Buratai ya yi wannan zaburarwar ne yayin da ya kai ziyara sansanin soji da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Ya ce rundunar sojin ba za ta bawa masu aikata laifuka damar su numfasa ba. Buratai ya yi wannan jawabin ne a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari na jihar Katsina a yayin da ya kai ziyarar duba yadda aikin rundunar Operation Sahel Sanity da aka kaddamar a Arewa maso Yamma ke tafiya.