Bashin da Najeriya ta ciwo ya kai naira tiriliyan 31 – DMO


Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa (DMO), ta ce bashin da ake bin Najeriya zuwa watan Maris ya kai naira tiriliyan 31 (wato dala bilyan 85.897).

Ofishin ya ce adadin ya kai naira tiriliyan 31 din ne bayan da aka kara rikito bashin tiriliyan 2.38 na naira, kwatankwacin dala bilyan 6.593 ya zuwa watan Yuni da ya gabata. Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (Debt Management Office) ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

DMO ya ce tulin bashin ya kara hawa sama ne daga naira tiriliyan 28.628 zuwa naira tiriliyan 31.009 a watan Maris.

Ofishin DMO ya rarrabe yadda bashin ya rika hauhawa daga wanda aka ciwo a hannun Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), sai kuma wani saura da aka ciwo domin kokarin cike rarar ayyukan da aka gindaya alƙawurran za a yi, a cikin kasafin kudi na 2020.

Sabon bashin da ake bin Najeriya na cikin gida sun hada da: naira bilyan 162.557 daga kuɗin Sukuk da gundarin alƙawarin kidade a rubuce da Najeriya ta bayar, domin a biya masu shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.