Buhari Ya Umurci Ministocinsa Da Su Dinga Tallata Ayyukan Da Gwamnatinsa Take Yi Wa Al'umma

Buhari Ya Umurci Ministocinsa Da Su Dinga Tallata Ayyukan Da Gwamnatinsa Take Yi Wa Al'umma Domin 'Yan Adawa Su Ji Kunya

 

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi kira ga ministocin sa su maida hankali sosai wajen tallata ayyukan raya kasa da raya al’umma da gwamnatin sa ta samar.
Ya ce su maida hankali sosai kada su yi sanyin jiki har masu adawa da wadanda ba su fatan alheri a gwamnatin sa su rika watsa surutan da za su dusashe hasken tauraron gwamnatin sa.