Gidauniyar Bill Da Melinda Gates da Ta Dangote sun yaba da abinda suka ce namijin kokarin ne, da gwamnatin jihar Yobe ta yi na dakile cutar shan inna (Polio). Wannan yabawar ta fito ne a wata takardar da Mamman Mohammed ya sanya wa hannu, inda ya mika ta ga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN), a yau Asabar a garin Damaturu.
A cikin takardar Mohammed ya shaida cewa Bill Gates da Alhaji Aliko Dangote sun yaba da kokarin da gwamnatin jihar ta yi na kawo karshen cutar, a cewarsu wannan ba karamin abun a yaba bane, duba da yadda jihar ta Yobe take fuskantar matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya.
Sun jadadda jinjina ga wannan namijin kokarin, inda suka ce ya taimaka matuka wajen kawo karshen gaba daya a Nijeriya, sannan Bill Gates ya karawa gwamna Buni karfin gwiwar ci gaba da yakar cutar, da ma sauran cutukka da suke addabar al’umma. Haka shima Dangote Karin karfin gwiwa ya yi wa gwamnan Jihar.