Don Kariya Daga Yaduwar Cututtuka Ya kamata A Tsaftace Tsoffin Jarkoki Da Ake Zuba Abubuwan Sha – Dokta Bashir Bala Getso.

 


Yanzu haka dai al’adar nan da ta game gari ga masu sana’ar yin ababen sha a gidaje kamar zobo, kunun aya da kunun zaki da ake amfani fa tsoffin robobi ko jarkoki da ake zubawa a sayar hakan na tattare da hadarin kamuwa da cututtuka.
Wani bincike da muka gudanar yawanci irin wadannan jarkoki na Lemuka ne ko ruwan roba da ake a kamfanoni bayan an yi amfani dasu an zubar ko a gidajen buki ko bola sai a rika tattarawa masu irin wadannan sana’oi suna saye suna zuba abin da suke sarrafawa.
Yawanci ana gani irin wadannan jarkokin basa samun kulawar da ta kamata wajen tsaftacewa idan aka yi la’akari da wasu a bola aka samo wasu kuma a gidajen buki ko wajen cin abinci aka samo sai kawai a girgijesu da ruwa a zuba abinda akeyi na sha da ake sayarwa jama’a da hakan kan iya jawo ko sabbaba yaduwar cututtuka.
Hakan ya sa mun tuntubi Dokta Bashir Bala Getso Shugaban kwalejin Kimiyyar lafiya da fasaha da tsaftar Muhalli
a jihar Kano wanda ya bayyana cewa za’a iya samun matsaloli na kamuwa da cutuka kamar na amai da gudawa.
Yayi nuni da cewa za’a iya samun zaunannun cututtuka da zai haifarda cutar zazzabin Taifod da kuma cututtukan cikin ciki.
Dan haka Dokta Bashir Bala Getso yace yakamata mutane su rika kulawa wajen amfani da irin wadannan jarkoki ko robobu in zasuyi amfani dasu bai dace ace kawai an dan zuba ruwa an girguje suba kadai shikenan a cigaba da zubawa mutane abinsha ana amfani dashi.
Dokta Bashir Bala Getso yace akwai hanyoyin tsafta da yawa da yakamata masu irin wadannan sana’oi a robobi subi wajen kyautata tsafatace su ta hanyar wankesu da sinadarin ‘bleach’ a sakasu a ciki a wanke da kyau sannan a adanasu a wajen da berayi ko kyankyasai ba zasu iya kaiwa garesu ba hakan zai taimaka in za’ayi amfani da tsofaffin robobin wajen rage kaifin kamuwa da cututtuka.
Dokta Bashir Bala ya ce yana da kyau mutane su kiyaye da kulada lafiyarsu a kowane lokaci domin lafiya abune mai mutukar tsada sosai