Ministar kudin Nijeriya, Hajiya Zainab Ahmad ta bayyana cewa tabbas farashin kayan abinci kara sama yake yi, ministan tayi wannan ikirarin ne bayan da Hadimin Shugaban Kasa na musamman a bangaren watsa labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya yi a makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa farashin ya fara sauka. Zainab ta bayyana haka a wani shirin safe da gidan talbijin din NTA ya yi da ita a safiyar yau Litinin.
Amma ta ce karin farashin man fetur ba zai shafi na kayan abincin ba, saboda mafiya yawan manyan motocin da suke jigilar kayan abinci a fadin kasar nan, ba da man fetur suke aiki ba, sannan ta bayyana cewa tallafin gwamnati zai yi matukar amfani a wasu fannoni ga ‘yan Nijeriya, musamman a wannan lokacin.
‘Tabbas farashin kayan abinci yana hauhawa, a kan kayan abinci yafi kamata a sanya tallafi ba a kan abubuwa irin man fetur ba, misali in ka sa mai a motarka kona shi zaka yi, ka sake sanya wa ka kona. Amma hakan ba daya bane da kayan masarufi da duk al’ummar kasa suke amfani da shi.’ Inji Zainab Ahmad