Fadar shugaban kasa ta ce farashin kayakin masarufi ya fara saukowa sakamakon sauye-sauye a bangaren noma da Gwamnatin shugaba Buhari ta aiwatar.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka ta cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.
Ya ce sauye-sauye da Gwamnatinsu ke yi wajen bunkasa noma zai taimaka gaya wajen samar da wadataccen abinci ga al’ummar kasar nan.
Malam Garba Shehu ya kuma ce an rufe kan iyakokin kasar nan ne ba wai kawai don dakile ayyukan masu safarar shinkafa ko sauran nau’ikan abinci ba, a cewarsa rufe kan iyakokin ya kuma taimaka wajen dakile safarar makamai.