Gamayyar Kungiyoyin Matasan Jihar Kano Sun Fara Shirin Ganin Matashi Dan Uwansu Ya Zama Gwamnan Kano A 2023

 


Sheik Badaru Mu'az Kano, inuwa ba ki kyamar kowa! Gatan Matasan Arewa,
tsohon dan takarar Gwamnan Kano ne a jam'iyyar GPN, tsohon mataimaki na musamman ga Malam Ibrahim Shekarau.
A yanzu dan kasuwa ne a Cairo, yana kasuwanci yana hidimtawa jama'a,
cikakken dan APC wanda a yanzu yana taimakawa Ganduje ta fuskoki da dama.
Sheik badaru Mu'az wanda ya yarda da ingantar rayuwar wadanda ke bukatar taimako a ciki da wajen Nijeriya. Matashin malami, matashin dan kasuwa, gashi basiri, don haka shi ya fi dacewa da wakilcin al'ummar jihar Kano da ta rasa ingantaccen wakilci na zamani na tsawon Shekaru.
Wadannan na daya daga cikin dalilai da hujjoji da suka sa mu matasa da mata muka fara hada kai don ganin mun kawo ingantaccen canji, a wannan jiha mai albarka, don haka muna neman goyan bayan duk wani matashi.
Muna neman shawarar iyayenmu dattijai, muna neman goyan bayan iyayenmu mata, dama mata muna tare.
Saboda mun yi la'akari da wasu halayen na Sheik Badaru Mu'az ta fuskar rashin nuna isa da fifiko a cikin jama'a irin wannan kuwa shi ke karawa dan Adam farin jini da kwarjini a cikin Mutane. Tabbas, dagawa da ji ji da kai shi ke sa al'umma kauracewa mutum.
Shakka babu, Sheik Badaru Mu'az Kano mutumin kirki ne da ya fito gidan mutunci. Sannan a kashin kan sa ba shi da burin da ya wuce ribanya hidimar da ya yi a baya, da wacce yake kan yi a yanzu.
Ya shirya tsaf ya kara hidimtawa mutanan jihar Kano da arewa kai har ma da Nijeriya baki daya.
Allah muke roko ya cikawa wannan hazikin Malami kuma matashi burinsa, albarkacin wannan rana ta Juma'a.