Gwamnatin tarayya ta shelanta ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, a matsayin ranar hutu domin bukin murnar ranar samun ‘yancin kan kasar nan na 60.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.
Ya taya ‘yan Nijeriya murnar bukin wannan muhimmiyar rana, sannan ya
bayar da tabbacin aniyar gwamnati na farfado da dukkanin harkokin
tattalin arzikin kasar nan.
Aregbesola ya ce: “kasar da ke da yawan al’umma miliyan 200 masu hazaka matukar gaske.
’Yan Nijeriya su na nuna bajinta kamar zinare a sassan ilimi masu yawa
da harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire, fannin wakoki, shirya
fina-finai da al’adu.
“Shakka babu, mu ne jagaban kasashen bakaken fata a duk fadin Duniyar nan ba wai a Afrika ba kadai.
Ministan a cikin sanarwar wacce ya fitar ta hannun babban Sakataren
ma’aikatarsa, Georgina Ehuriah, yana cewa, a daidai lokacin da muke
bukin cika shekarunmu 60 da samun ‘yancin kai, akwai bukatar kara mayar
da himma sosai domin yakar annobar nan ta korona.
Mu na kuma taya daukacin ‘yan Nijeriya murnar bukin ranar samun ‘yancin
kai, ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya irin gudummawar da shugabannin
Nijeriya din na farko su ka bayar a kasar nan duk da bambance-bambancen
addini, harshe da ke a tsakaninsu, wannan bai sanya an samu sabani ba a
tsakanin su wajen samun ’yancin kan kasar nan.