Gwamnatin Tarayya Ta Amince A Kashe Dala Bilyan 1.95 Domin Fara Aikin Layin Dogo Daga Kano Zuwa Jamhuriyar Nijar
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Majalisar zartarwa ta tarayya, ta amince da kashe dala biliyan 1.95 don gina layin dogo daga Kano zuwa Dutse (Jigawa) - Katsina- Jibia - Maradi (Jamhuriyar Nijar).
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai na fadar Shugaban kasa bayanin sakamakon taron majalisar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta, a zauren Majalisar, da ke Abuja.
Ya ce majalisar ta kuma amince da kashe naira bilyan 3 don tsarawa, kerawa, samarwa, gwaji da kuma kaddamar da wata karamar hanyar jirgin kasa mai nauyin tan 150 na gaggawa da kuma dawo da hannayen jari.
"Wannan shine farkon bayanin da aka amince dashi ga Ma'aikatar Sufuri.
Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda shi ma ya yi jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron, ya ce majalisar ta amince da sayen kayyakin kwamfyutoci guda 1,800 na kwamfutar tafi-da-gidanka don jarabawar na’ura mai kwakwalwa a makarantun horar da Kwastam na Najeriya guda uku a Gwagwalada , Lagos da Kano, akan kudi N351million.
Ya bayyana cewa majalisar ta kuma amince da N197million don fadada tsarin kula da tsabar kudi na Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yadda za a bi ka’idojin lissafin ma’aikatan kasa da kasa (IPSAS).
Ya ce software, idan aka girka ta, za ta inganta ingancin Sashen Kwastam.
“A madadin Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren kasa ina son yin rahoto kuma cewa ta samu amincewar membobinta guda biyu.
“Na daya shine na siyan komputa dubu daya da dari takwas na kwamfutocin tafi-da-gidanka na makarantar horaswa da kuma jarabawar gwajin na’ura mai kwakwalwa a makarantun horaswa na Kwastam guda uku na Najeriya da ke Gwagwalada, Lagos da Kano kan kudi N351,540,000, tare da kammala wa’adin makonni shida.
“Babbar fa’idar wannan kwangilar ita ce cewa tana adana sashen da kudade masu yawa wajen daukar masu ba da shawara don horo da sauran ayyuka.
Mohammed ya ce majalisar ta kuma amince da kara kwangilar gina babban ofishin babban kamfanin hada-hadar Fasahar Man Fetur a Abuja, kan kudi N3,773,784,399.48, wanda ya daukaka amincewar farko ga kwangilar zuwa N14billion.