Gwamnatin Tarayya Za Ta Raba Sabbin Dogayen Motocin Sufuri Guda 2000 Domin Rage Radadin Hauhawar Farashin Mai Ga 'Yan Nijeriya
Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta kammala shirin raba motoci 2000 domin sufuri a fadin tarayya domin rage radadin tashin farashin man fetur kan yan Nijeriya musamman masu zama a karkara.
Ministan harkoki na musamman, George Akume, ya bayyana hakan a Abuja a taron tattaunawar da yayi da yan kungiyoyin hadaka.
A cewarsa, shirin zai gudana ne tsakanin ma'aikatarsa, ma'aikatar aikin noma da raya karkara da kuma wasu hukumomin gwamnati.
Akume ya ce an yanke shawarar bi ta hannun kungiyoyin hadaka ne saboda tabbatar da aiwatar da shirin, maimakon baiwa wasu daidaikun mutane bashi, wanda hakan zai jinkirta aiwatar da aikin.
"Abinda muka lura shine, idan aka baiwa daidaikun mutane bashi, dawowa da shi na matukar wuya, amma idan akayi da kungiyoyin hadaka, abin zai fi saukin lura." Akume yace
"Manufar wannan shiri shine tabbatar da cewa mutanen karkara na samun saukin sufuri, yanzu da aka samu tashin farashin man fetur."
"Muna sane da cewa wasu 'yan kasuwan motocin haya za su kara farashin hawa mota."
"Amma idan muka aiwatar da wannan shiri, mun yi imanin cewa zai rage tashin farashin don jin dadin al'ummarmu.
" Ya ce babu yadda kasar nan zata cigaba ba tare da Sufuri ba wanda shine dalilin da yasa shugaba Muhammadu Buhari ke aiki tukuru ta bangaren gyaran hanyoyi, jiragen kasa da na sama.