Ina kokarin ceto 'Yan Nijeriya Miliyan Dari daga cikin fatara da talauci a cewar Shugaban Kasa Muhammad Buhari
Ina Ta Kokarin Cika Muradina Na Ganin Na Ceto 'Yan Nijeriya Milyan Dari Daga Cikin Fatara Da Talauci, Cewar Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na kokarin cika muradin sa na ganin ya ceto mutum milyan 100 daga fatara da talauci. Ya kuma ce ko masu hassada sun san cewa gwamnatin sa ta taka muhimmin rawa a cikin wannan shekara daya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Buhari ya yi wannan bayani ne daidai lokacin da rashin aikin yi ke kara dumfarar ƴan Najeriya da dama, ƙarin kuɗin fetur, ƙarin kuɗin wutar lantarki da kuma hauhawar farashin abincin da talakawa ke yi, wanda a yanzu ke neman ya gagare su.
Buhari ya yi bayanin ne wurin rufe taron Sanin-makamar-aiki da aka shirya wa Ministoci, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati.
