Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dora laifi a kan shawarar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya zartar ta mika sunayen lauyoyi 11, domin nada su a matsayin alkalai a babbar kotun da ke babban birnin tarayya Abuja ga Majalisar Dattawa, domin tantancewa.
A cikin hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo, ya yanke a jiya Laraba,
kotun ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, yay i aiki ne a bisa saba wa
dokar sashe na 256 (2), ta tsarin mulkin Nijeriya a lokacin da ya aike
wa da majalisar dattijan da sunayen da majalisar alkalai ta kasa ta aike
masa fa su.
Mai shari’a Ekwu ya ce,ta yanda kawai shugaban kasa zai iya aike wa da
shawarar ta majalisar alkalan zuwa majalisar Dattijan domin a nada du a
matsayin alkalan babbar kotun shi ne in da a ce abin ya shafi nadi ne na
shugabannin babbar kotun kamar babban mai shari’a na babbar kotun.
Sai dai alkalin ya yi hukunci da cewa shugaban kasan ya saba wa sashen
na 256 (2) na tsarin mulkin, don haka ba za a rantsar da alkalan ba.
