Kungiyar "Arewa Media Writers" Ta Mika Ta'aziyar Rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris, Ga Daukacin Al'ummar Masarautar Zazzau Da Al'ummar Yankin Arewa


Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana mika sakon ta'ziyyar rasuwar Mai martaba sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris, wanda daya ne daga cikin manyan sarakunanmu na Arewa. 

Kungiyar "Arewa Media Writers" ta nuna alhininta game da rasuwar mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris, CFR wanda ya rasu a yau yana da shekaru 84.

Marigayi Mai martaba sarkin Zazzau fitaccen sarkine mai tawali'u wanda aka sanshi da fafutukar tabbatar da zaman lafiya, neman hadin kan zaman lafiyar Arewa da kasar Nigeria baki daya.

A duk tsawon shekaru 45 da yayi a matsayin sarkin Zazzau, an san mai martaba da wa'azi, nasihar zaman lafiya da kuma kawo cigaba da hadin kai, ba wai kawai iya tsakanin mutanen yankinsa ko jihar Kaduna ba, har ma da kasa baki daya.

Hakikanin gaskiya wannan rashi al'ummar yankin Arewa a kayi wa, ba iya al'ummar Jihar Kaduna ba.

Kungiyar "Arewa Media Writers" tana yiwa marigari mai martaba, Addu'ar Allah ya Jikanshi ya gafarta mishi kura kuranshi.