Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa siyar da abinci akan hanya nada matukar illa ga lafiyar dan Adam
Siyar da abinci akan hanya ya zama ruwan dare inda za kaga ana siyar da abincin a kusa da kwatoci ko tarin shara wanda hakan ke da matukar illa ga lafiyar dan Adam baya ga janyo cituttuka masu yafuwa
Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa siyar da abinci a gun da yake da kwata ko tarin shara na da matukar illa ga lafiyar dan Adam amma duk da haka wasu sunyi buris da kiraye kirayen da masana sukai
A zantawar mu da wata mai sayar da abinci akan hanya ta bayyana dalilin ta Na sayar da da abincin a kan hanya.
"Bani da kudin da zan karbi shago,saboda ko kaje karban shagon zasu ce maka dubu dari 150 a kowani shekara ,gashi banida karfi kuma da sanaar nan nake kula da yarana".
Da muka zanta da wasu matasa da muka riska a gurin wata mai saida abinci inda suka bayyana cewa
"Ina iya siyan abinci a ko ina, kuma naci a ko ina koda kusa da kududdufi ne "
"Bana iya siyan abinci a ko ina duk wuya kuma nakan jira naje gida sai na ci"
"Gaskiya ina cin abinci a ko ina saboda inka duba dakyau zakaga kusan ko ina akwai kwata ko tarin shara"
Akan haka ne muka tuntubi shugaban kwalejin koyar da tsaftar muhalli ta jihar kano wato Dr Bashir Bala Getso inda ya bayyana illolin da hakan kan haifar wa lafiyar dan Adam
"Yace yakamata ake kiyaye tsaftar abincin da ake ci domin rashin yin haka nada matukar barazana ga lafiyar Dan Adam domin ta hakanne aka fiya samun cututtuka kamar su amai da gudawa thypoid fever da dai sauran su"