Kungiyar masu sana’ar yin biredi ta, Association of Master Bakers, da ke sashen kudu maso yammacin kasar nan sun yi barazanar daina yin sana’ar yin biredin a dukkanin Jihohin da suke a karkashin wannan yankin na su, a bisa abin da suka kira da tsadar kayayyakin yin biredin. A cewar shugaban kungiyar na wannan yankin, Alhaji Abolusodun Salawu da shugaban kungiyar a Jihar Lagos, Ambassador Raji Omotunde, “lokaci na karshe da muka yi kari a kan farashin na biredi shi ne a shekarar 2016, amma a yau din nan farashin dukkanin kayayyakin da ake yin biredin da su sun tashi sosai.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da yin wannan sana’ar tamu a cikin tafka asara a kullum ba. a kowane lokaci idan muka yi Magana a kan tashin farshin kayayyakin yin biredi, fulawa, sukari, bota da sauransu. Masu samar da wadannan kayayyakin a kullum kokawa suke yi da cewa bas a samun kudaden canji ne kai-tsaye daga hannun gwamnati wanda hakan ne yake tilasta masu sayen dalar Amurka daga hannun ‘yan kasuwa.
“Don haka, muna yin roko ga gwamnati da ta taimaka mana kafin mu rufe gidajen yin biredin namu,” in ji shi.