Fitaccen dan siyasa, kuma mawakin siyasar nan da ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya,’ Malam Ibrahim Sale, wanda aka fi sani da Malam Yala ya ajiye mukaminsa.
Yala, wanda shine Mai ba Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honorable Yusuf Ibrahim Zailani shawara kan harkokin watsa labarai ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram a ranar Talata.
“A jiya 28 ga watan Satumba na 2020 ce na ajiye mukamina a matsayin Mai ba Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna shawara kan harkokin watsa labarai. Ina mai amfani da wannan damar domin godiya ga Shugaban Majalisar domin damar da ya ba ni na yin aiki a karkashinsa,” inji Yala.
Malam Yala dan siyasa ne a Kaduna, inda ya kasance Darakta Janar na Yakin Neman Zaben Sanata Uba Sani a zaben 2019.