Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani kwamiti na musamman wanda zai taimakawa Gwamnati wajen bunkasa harkar samar da wutar lantarki.
A cewar Shugaba Muhammadu Buhari kwamitin zai yi aiki tare da baiwa Gwamnati shawara kan yadda za a magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren wutar lantarki.
Mambobin kwamitin sun hada da Attorney Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami da ministar kudi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad da ministan samar da wutar lantarki Saleh Mamman, da kuma ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministan shari’a Abubakar Malami Dr Umar Lawan Gwandu, ta ce sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban hukumar sayar da kadarorin Gwamnati Mista Alex Okoh da kuma shugaban kungiyar Injiniyoyin Najeriya Babagana Muhammad.