Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ta kammala duk wani shiri da tsari da ake buƙata don tabbatar da an yi zaɓen gwamnan Jihar Edo cikin nasara a ranar Asabar ɗin nan.
Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.
Okoye ya ce INEC ta gama shirya wa zaɓen tsaf.
Ya ce duk wasu kayan aiki marasa haɗari da aka tanadar don zaɓen na Edo an gama kai su cibiyoyin zaɓe tun cikin Agusta.
“Kayan aiki masu hatsari, wato irin su fom-fom na rubuta sakamakon zaɓe da kuma takardun ƙuri'u.
