Bayan nasarar da ya samu wajen shirya zaɓen gwamnan Jihar Edo a ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Hukumar zaɓen ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bada tabbacin cewa sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
Yakubu ya faɗi haka ne a Akure, babban birnin Jihar Ondon, a ranar Laraba, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewar shugaban
ya je Akure ne don ziyarar kwana uku saboda duba shirye-shiryen da
ofishin hukumar ke yi don gudanar da zaɓen, ya kuma gana da masu ruwa da
tsaki a zaɓen.
Farfesa Yakubu, wanda ya ce ya je jihar ne domin ya sadu da ma’aikatan
hukumar da ke jihar, ya ƙara da cewa duk da matsalar gobara da aka samu a
ofishin INEC na jihar, hukumar ta gama duk wani shiri saboda zaɓen.
Ya ce: “Mun riga mun murmure. Sai dai abin baƙin ciki shi ne mun yi
asarar injinan karanta katin zaɓe masu aiki da ƙwaƙwalwa har guda 5,000
amma mun murmure ta hanyar sake samo injinan da ake buƙata daga Jihar
Oyo da ke maƙwabtaka da nan, kuma an kawo su nan.
“Sun iso, an yi cajin su kuma an yi masu saiti, an shirya su domin zaɓen da za a yi a ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo.
“Abu muhimmi shi ne za mu yi amfani da komfutocin ‘Z-pads’ wajen tura
sakamakon zaɓen kai-tsaye a ranar zaɓen, kuma mun ɗauko waɗannan
‘Z-pads’ ɗin daga Edo zuwa Jihar Ondo saboda zaɓen.
“Saboda haka, irin shirye-shiryen da mu ka yi a Edo, su ne kuma mu ka yi a Ondo, saboda haka mun shirya wa zaɓen.”
Yakubu ya ce zai haɗu da majalisar sarakunan gargajiya da hukumomin
tsaro da jami’an hukumar a Yankunan Ƙananan Hukumomi 18 da ke jihar
musamman saboda zaɓen.
Ya ce, “Wannan ita ce ziyarar farko da na kawo. Za mu sake dawowa bayan
mako ɗaya don babban taro da za mu yi da masu ruwa da tsaki da kuma
rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.”
INEC dai ta yi asarar komfutocin karanta katin zaɓe guda 5,141 da za a
yi amfani da su a zaɓen na ranar 10 ga Oktoba a Jihar Ondo lokacin da
wuta ta tashi da dare a ofishin hukumar a Akure.
