Mutum 2,500 sun rasa Muhallinsu A sanadiyar ambaliyar ruwa a Jihar Kwara

 


 Akalla Sama da mutum 2,500 ne suka rasa muhallinsu sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a cikin kwanakin nan a jihar Kwara, an yi ambaliyar ne a garin Jebba da ke karamar hukumar Moro ta jihar Kwaran. Ruwan sama ne ya haifar da ambaliyar kamar yadda dan majalisar jiha mai wakiltar yankin ya shaida.

Ambaliyar ta share gonaki, da amfanin gonakin, an tabka asara sosai a cewar dan majalisar, zuwa yanzu ba a kai ga tantance irin asarar da aka yi ba, amma dai an bukaci al’ummar yankin da su yi hakuri, gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen tallafa musu.