Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa 'Kasar nan zata gyaru ta tsaya da kafarta fiyeda yadda take a yanzu
Buhari ya fadi haka ne a cikin wata shimfidar Littafin Nijeriya ta cika
shekaru 60 da Kamfanin LEADERSHIP COLLECTION, wani bangare na
Rukunin LEADERSHIP ya tattaro.
Littafin, wanda za a buga nan ba da jimawa ba, ya sanya farin ciki a cikin jama’a da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Wasu masu yin rijistar sun danganta kokarin a matsayin muhimmiyar alama
don bikin zagayowar ranar 1 ga Oktoba da Nijeriya ta samu ‘yancin
kanta.
A cikin wani dan bangare da aka fitar a jiya Litinin, mai taken “Za’a
Iya Yin karfi In Ana Tare”, Shugaba Buhari ya ce, “ Na yi imabi cewa,
har yanzu Nijeriya tana da kyakkyawar makoma.
Inda ya kara da cewa, daga mawuyacin halin da muka shiga a baya, har
yanzu akwai yiwuwar a iya hadin kai don tabbatar da kasa daya da duk za
mu yi alfahari da ita, da ban yi yakin basasa ba na kuma zama shugaban
kasa na mulkin soji na dan takaitacen lokaci na kuma yi takara har sau
hudu don zama Shugaban kasa na dimokiradiyya. ”
Buhari ya bayyana kansa a matsayin “mai kyakkyawar fata, wand ya zabi
ganin tafiyar Nijeriya a cikin shekaru 60 da suka gabata kamar rabin
cika.”
Ya ce duk da cewa wasu na iya yanke kauna saboda kalubalen da ke faruwa
a yanzu, inda ya ce, yana da yakinin cewa, ayyukan da iyayenmu suka
kafa da kuma gwarazan da suka gabata ba za su zama a banza ba. Kamar Yadda Jaridar Leadership Hausa ta rawaito