Ra'ayin Comr. Sani Ismail (Al-Gusaweey)
Babu shakka sanin kowa ne irin rawar da sashen rundunar hana fashi da makami ta SARS ke takawa wajen samun zaman lafiya mai dorewa a yankin Arewa dama Najeriyya baki daya.
Duk da kalan wannan rawar da suke takawa bai hana a samu wasu bara gurbi daga cikin jami'an sashen SARS dake aiki bata hanyar daya dace ba wanda wannan ana samun shi a kowace hukuma.
Nasan duk wani mai bibiyan abubuwan da suke faruwa a kafafen yada labarai yasan irin nasarori da wannan sashe na hana fashi da makami ta SARS ke samu musamman a Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas akan yaki da ta'addanci.
Inyya tabbata cewa wasu dake cikin wannan sashe ta SARS sunyi laifi, kamata yayi gwamnati tayi musu gargadi aja kunnan su, sannan a nuna musu abun da sukayi ba daide bane maimakon ta amsa kiran masu zanga-zangar cewa a kawo karshen sashen SARS in.
Zanga-zangar a kawo karshen SARS bai rasa nasaba da wasu masu cin moriyar laifuka a Yankin Kudu domin su cigaba da cin karensu babu babbaka.
Anan jahar Kaduna duk wani mai aikata miyagun laifuka da yaji ance ga 'Yan Sandan SARS nan zakaga yayi maza-maza ya shiga taitayin shi, domin ya san basu da sauki inde akan aiki ne.
Ina amfanin rushe kalan wannan rundunar haka.....?