Shugaban Jam'iyyar PDP Ya ce, Ba Zasu Hana Atiku Takara A Zaben 2023 Ba

 


Ba Zamu Hana Atiku Takara A Zaben 2023 Ba, Cewar Shugaban Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar adawa ta PDP ta karyata zargin cewa ta yi watsi da dan takarar ta a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, domin zaben wani a 2023.

 
Daily Sun ta ruwaito cewa shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, ya karyata labarin bayan ganawarsa da wasu gwamnonin jam'iyyar a jihar Bauchi.
Secondus ya ce jam'iyyar za ta tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci takara zai iya ba tare da tsangwama ba.
Yace: "Wannan jam'iyyar tana abubuwanta a demokradiyyance ne. Babu nuna wariya.
Duk wanda ya cancanta, tsoho ko yaro, gwamna ko tsohon gwamna, zai samu daman takara.