Daga:- Aliyu Adamu Tsiga
Da Sunan Allah mai Rahama mai jin kai Dukkan Yabo Ya Tabbata Ga Cikamakin Manzanni Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah Su Tabbata a Gare shi da Ahlinsa.
.
Allah ne Shaidana a Tsawon Rayuwata nayi Gwagwarmaya da Makiya Islama Domin Tabbatar da Tsaro a kasata Iraki.
Da Yawa daga cikinku Sun Butulce mun Inda a Yanzu Suke Murnar Mutuwata.
Amma lokaci zai zo da za kuyi Nadamar
Rashina Ku kuma Shugabannin kasashen Musulmai kun bada Ni Hadaya ga Azzaluman kasashen Yamma Wadanda ke Cigaba da kashe Dubban Musulmai domin Tabbatar Manufarsu ta Mallakar Duniya.
.
To ku Sani cewa, ko ba Dade, ko ba Jima Zaku Zama Ababen farauta ga Wadanda kuka Marawa baya a Yau Wasu daga Cikinku na kokarin kawo mun Tallafi Amma su daina Domin na Mika Rayuwata Ga Ubangiji Na Sai ku Yi kokarin Ceto na ku Rayukan da kuma hana
Rabuwar kasar Iraki.
.
Ya ku Yan Uwana Musulmai na Duniya ku Gaggauta hada kawunanku ko kuma ku Zama Tamkar kwallo a Hannayen Amurka da kawayenta Allahu Akbar ! Allahu Akbar !
Babu Wani abin Bauta Sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzonsa".
Allahu akbar, Ya Allah kajikan Saddam Hussain ka Yafe masa kura kuran sa.