Shugaba Buhari ya haramtawa duk wani likita fita Ƙasashen waje domin yin aiki


Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta yi duk abin da za ta iya wajen hana likitocin kiwon lafiya barin kasarnan.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a Abuja bayan ya duba aiki a sabuwar cibiyar kula da cutar kansa a Asibitin Kasa, dake Abuja.

Ehanire ya bayyana cewa gwamnatin da Muhammadu Buhari ke jagoranta za ta samar da abubuwan da za su taimaka wa likitocin su zama a ƙasar Domin bunƙasa lafiya.

Ministan Lafiya ya yarda cewa likitocin da suka bar Najeriya zuwa kasashen waje sun zama kalubale ga harkar kula da lafiya a Najeriya.

 "Muna da shirye-shirye don samar da ingantaccen kudade ga asibitocinmu a Najeriya da kuma kawo ƙarshen irin wannan ci-rani mara kyau," in ji shi.

 A cewar Ehanire, asibitoci sun yi rawar gani a lokacin da cutar COVID-19 ta yi kamari a kasar

Don haka, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa likitoci za su fi so su ci gaba da aiki a kasarnan a Maimakon Yadda suke sulalewa zuwa ƙasashen waje. 

 Ehanire ya shawarci manajojin asibiti da su kashe kudi yadda ya kamata, su kula da kayan aiki yadda ya kamata kuma su nemi wasu hanyoyin samun kudade domin ci gaba da lura Da Ma'aikatan. 

 Ya yaba wa masu kula da asibitocin kan irin hidimar da suke yi wa marasa lafiya cikin gaggawa sannan ya shawarce su da su kasance cikin shiri domin yiwuwar sake bullar cutar ta COVID-19 kamar yadda sauran kasashe ke fuskanta a yanzu.

 "Makarantu suna dawowa, mutane suna tafiye-tafiye ciki da wajen kasar don haka dole ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana, inji shi.